Karfe 3 na dare, wata baƙar mota kirar Lexus tayi parking a bakin gate ɗin makabarta.
Wasu samari guda 3 suka fito fuskokinsu a lullube, hannuwansu riƙe da ƙananan bindigu. Bayan sun fito, suka mayar da bindigunsu a aljihu suka durfafi bakin gate ɗin.
Sukayi knocking amma shiru. Sai da wani ya kara kwankwasa sannan wani dattijo mai gadi ya taso a firgice.
"Su waye?" ya tambaya.
Wani daga cikinsu yace, "Baba mai gadi, ka buɗe ƙofar, baƙi ne suka zo. Ɗan uwansu ya rasu cikin wannan daren, suna son su binne shi."
Sai mai gadin yace, "Ya ku yan samari, ku dai faɗi gaskiya. Duk wanda yake da gaskiya, ko da uwarsa ce ta rasu, ba zai zo makabarta irin wannan lokacin ba."
Da suka ga ba zai buɗe ba, suka yi haushi. Duk suka yi tsalle suka shiga cikin makabartar, suka daure mai gadin a jikin gate.
Suka nufi wani sabon kabari. Kafin minti 2 sun buɗe kabarin, suka ciro wata sabuwar gawar mace. Mutum 2 suka dauko gawar, daya yana biye da su a baya.
To, a daidai inda suka daure mai gadin ne yake kallonsu. Shi ma akwai karamar bindiga a jikinsa, amma daurin ya hana shi motsi. Cikin ikon Allah, hannu daya ya fice daga igiyar.
A lokacin da suke kokarin sanya gawar cikin motarsu, dattijon ya zaro bindigarsa a duhu ya saita inda suke sannan ya saki harbi...
ME YA FARU? Shin harbin ya same su? Me suka yi da gawar macen?
You must be logged in to post a comment.